Abubuwa sai Lahaula a Saudiyya: An kama babban Malami a Saudiyya da ya nuna rashin jin dadin shi dangane da badalar da ake yi a kasar

Abubuwa sai Lahaula a Saudiyya: An kama babban Malami a Saudiyya da ya nuna rashin jin dadin shi dangane da badalar da ake yi a kasar

- An kama wani babban Malamin addinin Musulunci a kasar Saudiyya saboda ya nuna rashin goyon bayan shi akan badalar da ake yi yanzu a kasar

- Malamin dai ya shiga hannu ne bayan wani bidiyo da ya saki ya bazu a duniya wanda yake nuni da irin yadda yake Allah wadai da abubuwan da suke faruwa a kasar

- Idan ba a manta ba kasar Saudiyya dai yanzu ta dage a kokarin da take yi na ganin ta kawo cigaba a kasar, inda take gayyato manyan mawaka na duniya suna holewa

An kama Farfesa Sheikh Omar Al-Muqbil, babban Malami a jami'ar shari'a ta Qassim dake kasar Saudiyya, an kama shine bayan ya nuna rashin jin dadinshi dangane da badalar da ake yi a kasar ta Saudiyya, inda ya nuna cewar wannan abubuwa da ake yi yanzu suna iya shafar al'adar kasar.

Wata kungiya mai bin hakkin mutanen da aka daure a gidan yari ita ce ta bayyana cewar an kama Muqbil din a shafinta na Twitter. A yadda Al-Jazeera ta ruwaito, kungiyar ta bayyana cewa an kama Malamin ne bayan wani bidiyo da ya saki yayi ta yawo wanda yake nuni da yadda ya nuna rashin jin dadinshi dangane da abubuwan da suke faruwa a kasar.

KU KARANTA: Tirkashi: Zaku zageni ku ci banza, amma baza ku taba Kaduna ku kwana lafiya ba - El-Rufai yayi gargadi

A 'yan shekarun nan dai kasar ta Saudiyya na ta gayyatar manyan mawaka na duniya irinsu, Mariah Carey, Janet Jackson, Sean Paul da sauransu, a kokarin da take na ganin ta kawo cigaba a kasar a idon duniya.

A shekarar da ta gabata kasar ta Saudiyya ta bayyana shirinta na sanya dala biliyan sittin da hudu ($64b) domin kawo abubuwan more rayuwa a kasar.

Bayan haka kuma an kama manyan Malamai da yan jarida da suka nuna rashin goyon bayansu akan abinda Yariman kasar Mai jiran Gado Mohammed bin Salman yake yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel