Kotun zabe ta tabbatar da nasarar 'yan majalisar Kano Jibrin da Gaya

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar 'yan majalisar Kano Jibrin da Gaya

Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisar jiha da na tarayya da ke zamanta a jihar Kano, ta tabbatar da nasarar Abdullahi Mahmud Gaya, a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisa mai wakilcin kananan hukumomin Albasu, Ajingi da kuma Gaya a majalisar tarayya.

A baya dai dan takarar kujerar na jam'iyyar PDP, Usman Mahmud Adamu, ya kalubalanci nasarar Abdullahi Gaya a gaban kotun sauraron korafin zabe dangane da babban zaben kasa na 2019 da aka gudanar, inda yayi ikirarin cewa zaben cike yake da mugudi da rashin gaskiya.

Kotun yayin zaman da ta gudanar bisa jagorancin Hon Jastis Ajoke Adepoju, ta tabbatar da nasarar Abdullahi Gaya wanda ya kasance dan takara na jam'iyyar APC.

Haka kuma ta yi watsi da korafin dan takarar PDP da cewa korafin sa bai karbu ba a sanadiyar rashin kawo madogara ta kwararan dalilai dangane da korafin da ya shigar.

A wani hukunci na daban da kotun ta zartar bisa jagorancin Jastis Nayai Aganaba, ta yi watsi da korafin Aliyu Datti Yako, dan takara na jam'iyyar PDP da ke kalubalantar nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Abdulmumin Jibrin.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na raba ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje - Buhari

Kotun mai sauraron kararrakin zabe, ta ce hakika Jibrin shi ne ya lashe zaben kujerar dan majaliar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Kiru da Bebeji na jihar Kano a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 27 ga watan Fabrairun 2019.

Tamkar hukuncin da kotun ta zartar a baya, ta ce Alhaji Datti ya gaza zayyana mata kwararan dalilai da za su zamto madogara ta korafin da ya gabatar a gabanta, lamarin da ya sanya ta fita batunsa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel