Ina jira naga dan iskan da zai zo yace mini nayi rijista kafin na cigaba da fim - Sakon Baban Chinedu ga Afakallahu

Ina jira naga dan iskan da zai zo yace mini nayi rijista kafin na cigaba da fim - Sakon Baban Chinedu ga Afakallahu

- A yayin da sauran jarumai ke ta faman tururuwa suyi rijista domin a tantance su a masana'antar Kannywood

- Shi kuma Baban Chinedu ya bayyana cewa sam-sam babu wannan maganar, domin kuwa ya caccaki shugaban tace fina-finan

- Jarumin ya ce yana nan yana jira yaga dan iskan da zai kirashi yace ya zo yayi rijista

A yayin da sauran jaruman Kannywood manya da kananan su suke ta faman tururuwa domin suje su bi umarnin shugaban kungiyarsu ta Kannywood a bangaren tace fina-finai, wato Isma'ila Na'abba Afakallahu, akan maganar da yayi ta cewa dole sai kowa yaje an tantance shi kafin ya cigaba da wasan fim.

Shi kuma fitaccen jarumin barkwancin nan wanda ake kira da Baban Chinedu ya bayyana a wani sabon bidiyo, inda ya nuna sam babu wannan maganar a tsarin shi, har ya bayyana cewa yana jira yaga wanda zai zo yace mishi yayi rijista kafin ya cigaba da wasan fim.

KU KARANTA: An gudu ba a tsira ba: Daga zuwa kai wa barayi kudin fansa shima anyi garkuwa da shi

Ga abinda jarumin ya ce a bidiyon:

"Hmmm! na sake dawowa, kuna ganin dan malamanku da bokayenku sunje sunyi muku aiki zan daina magana ne, ko kadan bazan daina magana ba na danje hutun rabin lokaci ne kamar yadda 'yan kwallo suke yi.

"Wai mu zo muyi rijista? Kai ka isa kai din banza kai wanene kai, ka manta lokacin da kace da bakinka ba sai jarumi yayi rijista ba, wato yanzu da yake lokacin siyasa ne, kuna so ku ci kudin mutane kuma ku dinga juya su yadda kuke.

"Mu muna karkashin kungiyar Kannywood ne ba karkashin kungiyar tace fina-finai ba, dama ina so na gargade ka, kana zuwa kana cewa mutane kai ne shugaban 'yan fim, ka daina yiwa mutane karya, saboda muna da shugabannin mu, saboda haka kada ka kara zuwa ka yiwa mutane karya.

"Yanzu kuma kirkiro cewa azo ayi rijista, muna nan muna jira, ni ina jira naga wanda zai kirani a waya yace Baban Chinedu kazo kayi rijista, wannan rainin wayo ne, so kuke ku kashe kungiya kowa ya dawo karkashin ku kenan," in ji babban jarumin barkwanci Baban Chinedu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel