Yan sanda sun kashe mutane 12 a lokacin tattakin Ashura, Inji kungiyar IMN

Yan sanda sun kashe mutane 12 a lokacin tattakin Ashura, Inji kungiyar IMN

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta bayyana cewa yan sanda sun kashe mambobinta akalla guda 12 a fadin kasar, yayinda suke tattakin Ashura a ranar Talata, 10 ga watan Satumba.

Sunyi zargin cewa an kashe su ne a lokacin tattakin a jihohin Kaduna, Bauchi, Gombe, Sokoto da Katsina.

Kakakin kungiyar, Ibrahim Musa, yayi bayani a wani jawabi cewa an kashe yan Shi’a uku a Kaduna, yayinda aka raunata wasu 10, haka zalika an kashe wasu uku a Azare, jihar Bauchi.

Ya kara da cewa an kashe uku a jihar Gombe.

Jawabin ya kuma ce an kashe mutum guda a Illela, yayinda aka kuma kashe wani a Goronyo duk a jihar Sokoto.

Ya kara da cewa an kashe wani dan Shi’a a Malumfashi da ke Katsina, inda yace da dama sun ji rauni sakamakon harbin bindiga a lokacin da yan sandan suka bude wa masu tattakin wuta.

KU KARANTA KUMA: Sanatan Plateau: Jam’iyyar PDP tayi gagarumar nasara a kotun zabe

A halin da ake ciki, mun ji cewa hankula sun tashi, jama’a sun shiga dimuwa yayin da wasu ayarin yan shia suka yi gaba da gaba da jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bauchi a garin Bauchi a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne da misalin karfe 10 na safiyar Talata a daidai shatale talen babbar kasuwar garin Bauchi da kuma Tashan Babiye, duk a cikin garin Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel