Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Kotun sauraron karrakin zabe na jihar Kano ta soke zaben Munir Dan'Agundi, dan majalisa mai wakiltan mazabar Kumbotso a majalisar wakilai na tarayya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan karar da Umar Ballah na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya shigar na kallubalantar nasarar Mr Dan'Agundi kan rashin samun kuri'u mafi rinjaye kamar yadda doka ta tanada.

DUBA WANNAN: Ashura: Mun gano makarkashiyar da gwamnati ta shirya mana - 'Yan Shi'a

A yayin da kotun ta ke yanke hukunci a ranar Talata, ta bayar da umurnin a jingine zaben Mr Dan'Agundi tare da bayar da umurnin sake sabon zabe a akwatin zabe na Tsamiya da ke mazabar Mariri.

Ku biyo mu domin samun cikaken bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel