Tsohon shugaban Najeriya Jonathan zai ziyarci kasar Mozambique

Tsohon shugaban Najeriya Jonathan zai ziyarci kasar Mozambique

An sa ran tsohon shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, zai fice daga kasar nan domin halartar taron kasa-da-kasa inda zai gabatar da jawabai kan tattalin arziki da za a gudanar a kasar Mozambique.

Taron wanda jaridar sha'anin kudi ta duniya wato Financial Times ta dauki nauyi, zai gudana a ranar Laraba cikin birnin Maputo na kasar Mozambique kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito.

An tattaro cewa, taron wanda shi ne karo na hudu cikin jerin gwanon taruka makamancin sa da suka gudana a baya, jaridar Financial Times mai tushe a birnin Landan, tana maraba da zuwan tsohon shugaban Najeriya domin gabatar da jawabai kamar yadda ta wassafa a wani sako a shafin sada zumunta na Twitter.

Ana sa ran tsohon shugaba Jonathan zai gabatar da jawabai dangane da kwarewar da ya samu a kan dokoki da tsare-tsaren tattalin arziki, cikin akidun tsohuwar gwamnatinsa musamman a fannin makamashi domin al'ummar kasar Mozambique su ribata.

Cikin sanarwar da jaridar Financial Times ta gabatar, ta ce babban taron na tattalin arziki da za a gudanar a kasar Mozambique zai samu halarcin manyan ministoci, masu kawo tsare-tsare, da kuma shugabannin gida na waje kan harkokin kasuwaci da kuma sauran masu ruwa da tsaki, inda za a tafka muhawara da shimfida sabbin shawarwari a kan bunkasa tattalin arziki.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, daga karshe gaskiya ta bayyana dangane da dalilai da suka sanya tsohon shugaban kasa GoodluckJonathan, bai hukunta Janar Muhammadu Buhari ba, wanda a wancan lokaci ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC duk da haifar da rikicin da yayi a fadin kasar nan, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama bayan babban zaben kasa na 2011.

Cikin wani sabon littafi da ya wallafa a kan nauye-nauyen da suka rataya a kan tsaffin lauyoyin koli na Najeriya, tsohon lauyan koli kuma ministan shari'a na Najeriya, Muhammad Adoke, ya bayyana dalilai da suka sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwana lafiya bayan haifar da tarzoma a kasar nan da ta salwantar da rayukan mutane da dama a zaben kasa na 2011.

KARANTA KUMA: A tashi a farga a kan harkar ilimi a Najeriya - ASUU

Tsohon ministan shari'ar kasar ya ce, neman a zauna lafiya ya sanya Buhari bai fuskanaci wani hukunci ba duk da haifar da rikicin da yayi bayan babban zaben kasa na 2011, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama ciki har da wasu masu yi wa kasa hidima guda 12.

Adoke cikin sabon littafin da ya wallafa, ya ce yanayin rudani a kasar a wancan lokaci ya sanya gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta sauya ra'ayi inda ta fasa cafke Buhari tare da hukunta shi, domin kuwa a cewarta aiwatar da sabanin hakan zai iya kara jefa kasar nan cikin tashin-tashina.

Tsohon lauyan koli na kasa ya ce, muradin kwantar da tarzoma da neman a zauna lafiya ya sanya gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta fita batun Buhari ba tare hukunta shi ba. Ya ce hakan ya bayu ne a sanadiyar wani kwamitin bincike da hangen nesa da gwamnatin ta kafa bisa jagorancin fitaccen jagoran addinin Islama na Arewacin Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel