Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da Fastoci da Limaman da ke jefa Najeriya cikin rikici

Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da Fastoci da Limaman da ke jefa Najeriya cikin rikici

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi Allah wadai da fastoci da Limamai, wadanda ke ingiza tashin hankali da kuma shigar da siyasa cikin addini a Najeriya.

Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Satumba, a taron addinai da yayi da kiristoci da musulmai a Akure, babban birnin jihar Ondo.

An gudanar da taron kafin taron bikin Akure Ulefunta festival inda zai gabatar da jawabi a ranar Litinin.

Taken lakca shine: “Our Diversity, a Divine Gift and Blessings untapped: Wrong Path trodden and Way to Peace.”

Sarkin musulmin yace dole malamai su kange kansu su kuma lura da furucinsu yayin da suke yin wa’azi, saboda kada su rikitar da al’amura a kasar.

Ya kara da cewa abun bacin rai ne yanda wasu malamai suke amfani da damar mabiyansu wajen azurta kansu yayinda mabiya ke karewa cikin rayuwar talauci.

Yayi gargadi ga mabiya addinai da su daraja juna, inda yake fadin cewa “akwai dangantaka iri guda tsakanin kiristoci da musulmai” wanda ya kamata a yada don cigaban al’umma.

Abubakar ya jaddada muhimmancin hada kai wajen yin magana akan al’amuran da suka shafi kasar, saboda a samu sakamako karbabbiya.

KU KARATA KUMA: Ni ba makiyin addinin Musulunci bane - Wike

Sarkin musulmin ya karfafa cewa dole shuwagabannin addini su fadi gaskiya ga ga wadanda ke rike da mukamai, saboda hakan zai taimaka ma gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaituwa a Najeriya.

A nashi bagaren, Oba Aladetoyinbo Aladelusi, Sarki Akure ya yabi sarkin musulmi bisa rawar gai da ya taka wajen warware rikici a fadin duniya. Yayi addu’ar nasara ga ayyukan da sarkin zai gudanar a jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel