An sayar da Ibrahim Salisu Iriyos, dan kwallo mafi tsada kan N5,000 a Kano

An sayar da Ibrahim Salisu Iriyos, dan kwallo mafi tsada kan N5,000 a Kano

Rahotanni daga kasuwar musayar yan wasa sun kawo cewa an gudanar da wani ciniki mafi tsada a Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu, inda kungiyar kwallon kaa ta Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin.

Kungiyar ta Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta siya Ibrahin Iriyos daga kungiar Aston Villa ta Gano kan kudi naira dubu biyar.

Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha'awar komawa kungiyar Super Stars domin ci gaba murza leda, ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Villa Gano.

Hakan ya sa Iriyos kan je atisaye a kugiyar Super Stars a lokacin da kungiyarsa Aston Villa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake taka leda aka kuma cimma matsaya a sayo shi.

KU KARANTA KUMA: Talauci ya jefa wata budurwa cikin mawuyacin hali bayan saurayinta ya kasa biyan sadakin aurenta

Idin Gano shi ne shugaban Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Villa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel