Jihar Niger: Kotun zabe ta jaddada nasarar Sanata Musa

Jihar Niger: Kotun zabe ta jaddada nasarar Sanata Musa

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Minna, jihar Niger ta soke karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta a zaben da ya gabata, Ibrahim Isyaku (SAN) suka shigar, inda suke kalubalantar nasarar sanata mai wakiltan yankin Niger ta gabas, Sani Musa akan hujjar cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bata kasance da tsayayyen dan takara ba a zaben.

Sun yi zargin cewa Musa bai kasance da mafi yawan kuri’u ba a lokacin da shi da wani dan takarar jam’iyyar David Umaru suka tsaya takarar zabe a jam’iyyar APC.

Masu karar sun bayyana cewa matakin APC baya bisa ka’ida domin sun tsayar da yan takara biyu wanda hakan na nufin kuri’un yan takara biyu aka hade wa mutum daya.

Da yake zartar da hukunci a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba a Minna, shugaban kotun zaben, Justis Atinuke Oluyemi ta yi watsi da karar sannan ta riki cewa masu karar basu gabatar da kwakkwaran hujja domin tabbatar da cewar kuri’un da aka jefa APC na yan takara biyu ne.

Justis Oluyemi ta kara da cewar rashin sanya sunan David Umaru a cikin karar ganganci ne sosai domin cewa “babu ta yadda za ka yi wa mutum aski ba tare da ya kasance a wurin ba.”

Haka zalika, Justis Oluyemi ta tabbatar da zaben Sani Musa a matsayin sanata mai wakiltan yankin Niger ta gabas.

KU KARANTA KUMA: Bayan Mugabe, kasar Zimbabwe ta sake rashi na wani babban jigonta

Da yake martani akan hukuncin, lauyan masu kara, Mohammed Mohammed, yace za su daukaka kara akan hukuncin a kotun daukaka kara.

Lauyar Sani Musa, Amirah Abubakar ta nuna amincewa da hukuncin kotun zaben, inda ta nuna tabbacin cewa koda masu karar sun daukaka kara, sanatan ne dai zai kai labari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel