Toh fah: An gurfanar da wani malami akan satar babur a jihar Ekiti

Toh fah: An gurfanar da wani malami akan satar babur a jihar Ekiti

Rundunar ya sanda a jihar Ekiti, a ranar Alhamis, 5 ga wata Satumba, ta gurfanar da wani malami dan shekara 32, Opeyemi Sunday a gaban wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti kan zargin satar babur.

Dan sanda mai kara, Inspekta Caleb Leranmo, ya fada ma kotun cewa wandake karar ya aikata laifin da misalin karfe 12:30 na rana a ranar 25 ga watan Agusta a Afao-Ekiti, karamar hukumar Ifelodun/Irepodun da ke jihar.

Leranmo yayi zargin cewa wanda ake karan ya sace wani babur kirar Bajaj Boxer mara lamba, mallakar wani Yusuf Seyi.

Dan sanda mai karar yace laifin yayi karo da sashi 390 da dokar ta’addanci, Cap C 16, Vol. 1, dokar jihar Ekiti, 2012.

Sai dai kuma, Sunday bai amsa laifinsa sannan lauyansa, Mista Timileyin Omotosho, ya bukaci kotu da ta bayar da belin shi, inda yayi alkawari cewa wada yake karewa ba zai tsere wa beli ba.

KU KARANTA KUMA: Babban bankin duniya ya fasa kwai, yace Najeriya na mutuwa a hankali

Alkali Ade Lawal ya bayar da beli wanda ake zargin akan kudi N50,000 tare da mutane biyu da za su tsaya mai.

Ya dage zaman zuwa ranar 11 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel