Sojojin Najeriya sun kwato dabbobi 134 daga hannun barayi, sun mika ma gwamnati

Sojojin Najeriya sun kwato dabbobi 134 daga hannun barayi, sun mika ma gwamnati

Kwamandan Garrison na rundunar ta 1 na Sojan kasa ta Najeriya, Birgdeiya Jimmy Akpor ya mika ma jami’an gwamnatin jahar Kaduna shanu guda 134 da suka kwato daga hannun yan bindiga dake satar shanu a Kaduna.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba ne Birgediyan ya mika wadanna dabbobi ga wakilin gwamnatin Kaduna, kuma shugaban Operation Yaki na jahar, AIG Murtala Abbas a kauyen Kakau dake karamar hukumar Chikun.

KU KARANTA: An samu rabuwar kai tsakanin wasu yan madigo yayin da ‘Mata’ ta harbe ‘Mijinta’

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai shanu 120 da kuma awaki 14, wanda dukkaninsu an kwato su ne daga hannun wani kasurgumin dan bindiga mai suna Aminu Mallam, wanda ake ma inkiya da Baderi, wanda Sojoji suka kama shi a kauyen sabon Gayan.

“Akwai shanu 120 da awaki 14, sai kuma guda daga cikinsu da ta sau haihuwar yaya biyu da safen nan, mun lura cewa yan bindigan suna amfani da kananan yara wajen kiwon dabbobinsu da suka sata, ba tare da yaran sun san na sata bane, mun kama yaran, amma har yanzu bamu gano iyayensa ba.” Inji Jimmy.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban Operation Yaki ya bayyana cewa zasu mika dabbobin ga sashin binciken manyan laifuka na hukumar Yansandan Najeriya don gudanar da cikakken bincike kafin su mika ma masu dabbobin hakkokinsu.

“Za mu binciko masu dabbobin, sa’annan sai mun tabbatar da gaskiyar mutum kafin mu bashi dabbobinsa, za mu bukaci mu san lokacin da aka sace maka dabbobinka, adadinsu da dai sauran bayanai, kafin ma mu bari mutum ya yi ido hudu da dabbobin, idan mun gamsu zamu mika masa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel