Dubu ta cika: An kama wata mata a filin jirgi da sabon jariri a cikin jakar kaya

Dubu ta cika: An kama wata mata a filin jirgi da sabon jariri a cikin jakar kaya

- An kama wata mata da ta sanya jariri dan kwanaki shida da haihuwa a cikin jaka za ta gudu dashi

- Matar an kamata a filin jirgin sama ne na kasar Philippine yayin da take kokarin hawa jirgin da zai kai ta kasar Amurka

- Ma'aikatan filin jirgin sune suka gano cewa akwai jaririn a cikin jakar matar, sai dai kuma ta bayyana cewa dan uwanta ne

An kama wata mata 'yar kasar Amurka, an kuma tsare ta a kasar Philippine bayan ma'aikatan filin jirgin sama sun gano cewa akwai sabon jariri a jakar da ta zuba kaya a ciki, inda take kokarin barin kasar.

Wannan lamari dai ya faru ne a jiya Laraba da safe a filin jirgin sama na Ninoy Aquino dake Manila da misalin karfe 6:20 na safe.

Wani jami'in tsaro na kasar ya bayyana sunan matar da Jennifer Erin Talbot, wacce tayi kokarin fita daga kasar domin tafiya kasar Amurka, sai kawai aka ga sabon jariri dan kwanaki shida da haihuwa a cikin jakar kayanta.

KU KARANTA: Dan gidan tsohon shugaban kasar Misra Abdullahi Morsi ya mutu a asibiti dalilin bugun zuciya

Matar ta sanar da jami'an tsaro cewa yaron dan uwanta ne, sai dai kuma babu wata takarda da ta nuna hakan.

Har yanzu dai ba a fara gabatar da bincike akan ta ba, bayan ta bukaci cewa tana so tayi magana da jakadan kasar Amurka dake kasar.

Yanzu haka dai an dauki jaririn an kai shi wajen da za a kula dashi kafin a kammala bincike akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel