Thailand: 'Yan sanda sun yi taron dangi sun kama wani dan Najeriya da ya naushi dan sanda a Bangkok

Thailand: 'Yan sanda sun yi taron dangi sun kama wani dan Najeriya da ya naushi dan sanda a Bangkok

'Yan sanda a kasar Thailand sun kama wani dan Najeriya da ya ci zarafin abokin aikinsu yayin da yake kan aiki.

Dan Najeriyar mai suna Edalere Abioye ya naushi dan sandan ne bisa kuskure yayin da yake kokarin raba shi fada da mutumin da yake haya a gidansa.

Jami'an 'yan sanda sun yi taron dangi tare da yi wa Abioye rubdugu inda suka kama shi suka tafi da shi a yayin da yake kokarin gudu wa.

Jami'an dan sanda Col Jessada ya ce an yi mahawara mai zafi a tsakanin Abioye da mutumin da ya bashi hayar gida a kan biyan kudin haya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindigar Katsina: Su waye su?

A yayin da muhawarar da suke yi ta kara daukan zafi, sai Abioye ya kai wa maigidan hayar naushi, amma sai aka yi rashin sa'a naushin ya sauka a kan jami'in dan sandan da ya shiga tsakaninsu domin ya raba su.

Ana tuhumar Abioye da cin zarafin jami'an dan sanda yayin da yake kan aiki.

Labarin faruwar lamarin ya shiga kafafen yada labarai ne a ranar 2 ga watan Saumba bayan faifan bidiyon yadda afkuwar lamarin ya watsu a dandalin sada zumunta.

Akwai 'yan Najeriya da dama dake karatu a jami'o'i daban-daban dake garin Bangkok, babban birnin kasar Thailand.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng