Kin jinin baki a Afirka ta Kudu: Buhari ya gana da Osinbajo, da ministan harkokin waje

Kin jinin baki a Afirka ta Kudu: Buhari ya gana da Osinbajo, da ministan harkokin waje

A yanzu din nan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, sun shiga bayan labule dangane da tababar kin jinin baki da ake yi a kasar Afirka Ta Kudu, biyo bayan hare-haren da aka zartar kan 'yan Najeriya a kwana-kwanan nan.

Buhari, Osinbajo, da ministan harkokin waje yayin ganawa a fadar Villa
Buhari, Osinbajo, da ministan harkokin waje yayin ganawa a fadar Villa
Asali: Twitter

Buhari, Osinbajo, da ministan harkokin waje yayin da suke tsaka da ganawa a fadar Villa kan kin jinin 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu
Buhari, Osinbajo, da ministan harkokin waje yayin da suke tsaka da ganawa a fadar Villa kan kin jinin 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu
Asali: Twitter

Hadimin shugban kasa Buhari a kan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana hakan a shafin zauren sada na Twitter.

Mr Bashir ya jadadda kudirin gwamnatin tarayya na kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu.

Ga sakon da Bashir ya wallafa a shafin sa na Twitter:

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, tuni dai gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka Ta Kudu a kasar, Mista Bobby Moroe sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar da yake wakilta.

Haka zalika, ministan harkokin kasashen ketare, Mr Onyeama, ya gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talatar da ta gabata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

KARANTA KUMA: Buhari ya gana da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya

Mr Geoffrey ya ce gwamnatin Najeriya za ta dauki kwararan matakai kan harin da aka kai wa 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu a ranar Litinin, lamarin da ya ce ba za ta sabu ba domin kuwa da zafi-zafi ake dukan karfe.

A cewar ministan, daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka akwai batun hadin gwiwa a tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu, lamarin da Ministan ya ce zai bai wa jami'an tsaron Najeriya da ke ofishin jakadanci Najeriya a kasar Afrika ta Kudu damar aiki tare da takwarorinsu na kasar domin bayar da kariya ga 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Kazalika, gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkan 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel