Duniya ta zo karshe: An halatta aure tsakanin mutane da dabbobi a kasar Norway

Duniya ta zo karshe: An halatta aure tsakanin mutane da dabbobi a kasar Norway

- Wata kotu a kasar Norway ta halatta aure tsakanin mutane da dabbobi na gida

- Kotun ta bayyana cewa iya dabbobi na gida ne banda na daji da kuma na ruwa

- Yanzu haka dai an samu wata budurwa mai shekaru 23 wacce ta auri wani karenta da ta sanyawa suna Rudolf

A wani rahoto da wata jarida ta kasar Norway ta ruwaito a watan Mayun shekarar 2017, kasar ta Norway ta halatta aure tsakanin mutane da dabbobi da ake kiwo na gida (amma banda dabbobin daji dana ruwa).

Barbara, mai shekaru 23 wacce ta yi magana da manema labarai za ta zama mace ta farko da zata fara yin wannan aure tsakaninta da dabba.

Barbara Trudlosmek wacce ta nuna jin dadinta ta gabatar da mijinta Rudolf, wani kare da babu mai shi da ta tsince shi a watan Janairun shekarar 2015, wanda kuma ta nuna ta amince ya zama miji a gareta.

KU KARANTA: Emmanuel Nwude: Dan damfarar da ba a taba yin kamar shi ba a Najeriya, ya damfari wani mutumi ta hanyar sayar mishi da filin jirgin sama dungurungum

"Ni da Rudolf muna magana tsakanin mu, yana fuskantar duk abubuwan dake faruwa kuma ya san muhimmancin wannan aure namu, har ma ya zabi wanda zai zame masa babban aboki, Ceasar wani kare dan shekara daya da haihuwa."

Da 'yan jaridar suka tambayeta game da kwanciya irinta aure ta ce: "Abinda muke yi na da Rudolf akan gado ba damuwar ku bane! Ni ban damu da sai an kwanta dani ba, kuma mijina ma ya nuna babu damuwa. Mun samu fahimtar juna matuka kamar yadda sauran ma'aurata suke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel