Babbar magana: Majalisar dinkin duniya ta yi kira a kan a gaggauta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Babbar magana: Majalisar dinkin duniya ta yi kira a kan a gaggauta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Agnes Callamard, Wakiliya na musamman da ke aika wa majalisar dinkin duniya (UN) rahoto a kan kisa ba bisa ka'ida ba ya yi Allah-wadai da yawaitar aiyukan ta'addanci a fadin Najeriya.

Da take jawabi yayin taro da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Callamard ta ce akwai bukatar daukan matakan gagga wa domin kawo karshen aiyukan ta'addanci da suka yi sanadiyyar salwantar rayukan dubban jama'a a Najeriya.

Najeriya na fama aiyukan ta'addanci masu suna daban-daban da suka hada da; Boko Haram, rikicin makiyaya da manoma, garkuwa da mutane, 'yan bindiga da rikicin mabiya mazhabar Shi'a.

"Hankalina ya tashi matuka da abinda na gani a Najeriya. Akwai bukatar a dauki matakan gagga wa a domin kawo karshen aiyukan ta'addanci da suke kara mamaye Najeriya, musamman a cikin shekaru biyar da suka gabata zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: ICPC na daf da kwace miliyan N840 da ta gano a asusun tsohuwar alkaliya daga arewa

"Idan aka bar rikicin da ke faruwa a Najeriya ya cigaba a haka, ba tare da daukan mataki ba, lamarin zai shafi gaba daya kasashen Afrika saboda irin rawar da kasar ke taka wa a nahiyar," a cewar Callamard.

Kazalika, ta yi Allah-wadai da abinda ta kira 'mugunta da cin zali' da 'yan sanda da sojoji ke yi a fadin Najeriya da kuma tsarin 'kama karya'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel