'Yan bindiga: Sarkin Katsina ya bukaci jama'a su dukufa da addu'a domin samun tsaro

'Yan bindiga: Sarkin Katsina ya bukaci jama'a su dukufa da addu'a domin samun tsaro

A yayin da hare-haren 'yan bindiga ke kara tsanani a sassan jihar Katsina, sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir, ya bukaci talakawansa su dukufa da addu'a domin samun dauki daga Allah.

Mai martaba Kabir ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Katsina, jihar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayin gabatar da jawabi ga malaman addinin Islama.

"Mu na umartar jama'ar masarautar Katsina da su dukufa wajen gudanar da addu'o'i na musamman daga yau, domin samun kariya daga ubangiji daga kan 'yan bindiga da barayin shanu.

"Ya zama wajibi a matsayin mu na Musulmi, za mu dage da rokon Allah domin ya kawo mana karshen wannan masifa.

"Wadanan 'yan bindiga sun kashe min jama'a, sun sace mata da kananan yara. Ba nu da wani zabi da ya wuce mu rungumi addu'a, saboda addinin Musulunci ya koyar da mu cewa addu'a tana maganin masifa.

"Dolen mu gaba daya mu dage da addu'a. Addu'o'in mu zasu taimaki jami'an tsaro a atisayen da suke yi domin murkushe 'yan bindigar," a cewarsa.

Kazalika, sarkin ya yaba wa gwamnatin jihar Katsina bisa samar da taimakon ababen hawa ga jami'an tsaro da ke yaki da 'yan bindiga a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel