Tsohon shugaban kasar Sudan ya bayyana inda ya samo makuden kudaden da aka kama a gidansa

Tsohon shugaban kasar Sudan ya bayyana inda ya samo makuden kudaden da aka kama a gidansa

- Tsohon shugaban kasa Al-Bashir ya bayyana cewa Yarima Salman na kasar Saudia ne ya ba shi makuden kudaden da aka kama a gidansa

- A watan Yuni ne masu bincike suka kama buhuna maqare da kudaden kasar waje a gidan tsohon shugaban kasar Sudan

- Ya bayyana cewa bai kai kudin zuwa babban bankin kasar bane saboda karramawa ga Yariman na Saudiyya

A yayin zaman kotu a kan shari'ar tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir, ya bayyana cewa tarin makuden kudaden Yarima Salman na kasar Saudiyya ne ya ba shi kudin.

Mai shari'ar ya tuhumi tsohon shugaban da mallaka, tare da amfani da kudin ta haramtacciyar hanya, abinda tsohon shugaban ya musanta.

A lokacin da alkalin ya ke tambayarsa dalilan ajiye kudin a gidansa, ya bayyana cewa, yin hakan karramawa ce ga Yariman na Saudiyya domin shi ya bukaci hakan.

Ya ce: "Ba mu kai kudin babban bankin Sudan ba saboda muna da bukatar sirri. Kuma munyi hakan ne saboda hakan Yariman ya bukata."

KU KARANTA: Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta bayyana dalilan kama 'yan arewa 140 ma su shiga jihar

Ya kara da cewa, zai so a ce kotun ta sirranta zamansu kuma kada a bayyana sunan Yariman saboda baya son bayyanar sunansa. A don haka ne ma ya aiko da kudin a wani jirgi na daban da kuma jakada na musamman.

Tsohon shugaban kasar Sudan din ya amince da karbar miliyoyin kudin daga Saudiyya, amma lauyoyinsa sunce tuhumarsa da ake ba ta da tushe.

Idan zamu tuna, a watan Afirilu na wannan shekarar ne aka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Sudan din. Bayan wata da watanni da a kayi ana zanga-zanga, abinda ya kawo wa'adin mulkinsa na kusan shekaru talatin.

A watan Yuni ne, masu gabatar da kara suka ce sun gano buhuna makare da kudaden kasar waje a gidansa.

Sauran abubuwan da ake tuhumarsa dasu sun had a da haddasa rikici ta hanyar fusata jama'a da kuma hannu a kisan masu zanga-zanga.

Zargin sun taso ne daga binciken kisan da ake yi na likita da aka kashe lokacin zanga-zanga, hakan ne ya yi sanadiyyar zuwan karshen mulkin na Al-Bashir.

Masu rajin kare mulkin damokaradiyya na Sudan na farincikin cimma nasara bayan da sojoji suka amince da yarjejeniyar kafa mulkin farar hula.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel