Hadiza Gabon ta tallafawa Maryam KK da makudan kudade akan iftila'in da ta fada na shiga hannun 'yan bindiga

Hadiza Gabon ta tallafawa Maryam KK da makudan kudade akan iftila'in da ta fada na shiga hannun 'yan bindiga

- Jaruma Hadiza Gabon ta tallafawa jaruma Maryam KK da makudan kudade bisa iftila'in da ya fada mata na shiga hannun 'yan garkuwa da mutane

- Maryam dai ta shiga hannun barayin ne a lokacin da taje daukar fim a babban birnin tarayya Abuja

- Jarumar ta yi bayanin yadda barayin suka kama ta da kuma irin abubuwan da suka yi mata

A kwanakin nan muka samu wani mugun labari na wani iftila'i da ya fadawa daya daga cikin jarumai mata masu tasowa a masana'antar Kannywood wato Maryam KK bisa cafke ta da masu garkuwa da mutane suka yi akan titin Kaduna zuwa Abuja.

Sai dai bayan kwana biyu da bacewar ta jarumar ta bayyana wurjanjan cikin mawuyacin hali bayan dukan kawo wuka da masu garkuwar suka yi mata bayan sun kwace komai nata gami da yashe kudin bankin ta.

Manema labarai sun samu tattaunawa da jarumar inda ta labarta musu labarin faruwar lamarin kamar haka:

"Bayan mun gama aiki ne da su darakta Sunusi Oscar, sai na zo titin gefen tashar Jabi dake Abuja zan hau mota zuwa Mararraba/Nyaya. A lokacin da na shiga motar ni kadai ce, sai wani ma ya zo ya shiga sai kuma wani a kujerar gaba, daga nan sai muka soma tafiya duk da cewar motar ba ta cika ba.

"Bayan mun dauki hanya sai na ga sun canja hanya, amma kuma na gagara yin magana. Daga bisani kawai sai naji an shake min wuya tare da daure min fuska.

"Sai suka karbe min wayata da katin ATM dina guda biyu (dayan katin na yayana ne), suka duba kudin dake asusun ajiyata na banki, sai kuma suka soma kiran lambobin dake cikin wayata suna cewa ga halin da nake ciki don haka a turo musu da kudi ta asusun ajiya ta. Hakan yasa aka yi ta tura musu da kudi."

KU KARANTA: Yadda wani bawan Allah ya shafe shekaru 36 a gidan kurkuku, saboda ya saci N18,000

Maryam ta cigaba da cewa daga bisani kawai sai ta tsinci kanta a wani kango, inda ta tarar da 'yan mata da dama da wadannan matasa suka yi garkuwa da su. Kuma wadanda aka yi garkuwa da su din duka matane, babu namiji ko daya.

"Ni sun ma tausaya mini saboda basu azabtar dani sosai ba, amma sauran matan suna shan azaba, akwai wadda ma suka yi cinikin gabanta da nonuwanta za su sayarwa da matsafa," cewar Maryam.

KK ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun yi ikirarin cewa su dalibai ne kuma suna yin harkar garkuwar ne domin samun biyan kudin makaranta.

Jarumar ta cigaba da cewa daga bisani bayan sun kwace mata wayoyi da kudaden dake hannunta da na cikin asusunta da jakan kayan kwalliyarta na sama da dubu dari, sai suka dauko ta suka watsar da ita a yankin Area 1 dake cikin Abuja.

Bayan faruwar wannan lamari darakta Aminu S. Bono ya wallafa a shafinsa sakon godiya ga jaruma Hadiza Gabon inda ya ce ta aikawa da Maryam din makudan kudade wanda bai bayyana adadinsu ba gami da yi mata fatan alkhairi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel