Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya

Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya

Wata kungiya mai zaman kanta dake kula da ayyukan Hajji da Umra ta duniya, Hajji and Umra Forum ta karrama gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje sakamakon gamsuwa da tayi da kyakkyawan shirin da jahar Kano ta yi ma alhazanta a yayin hajjin bana.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Bashir El-Bash ne ya bayyana haka a shafinsa, inda yace shugaban kungiyar, Sheikh Muhammad ne ya yi wannan jinjina ga gwamnan Kano, tare da mika masa kyautan Al-Qur’ani mai girma da kuma kyallen dakin Ka’aba.

KU KARANTA: Babu wanda ya mari Sanata Babba Kaita a garin Kankiya – Hadiminsa

Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya
Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya
Asali: Facebook

Sheikh Muhammad, yace “Koƙarin da gwamnatin jahar Kano ta yi wajen kulawa da Alhazanta shi ne abin da ya sanya muka zabi mai girma gwamna don karrama shi da wannan lambar yabo ta musamman domin tabbatar masa da gamsuwarmu da shirinsa tare kara ƙarfafa masa gwiwar cigaba da kulawa da alhazan jahar.”

Wakilin Gwamna Ganduje a yayin wannan taron karramawa, Alhaji Abba Muhammad Dambatta, sakataren hukumar kula da jin dadin alhazai ta jahar Kano ya yaba kungiyar bisa wannan karramawa da ta yi ma gwamnan, sa’annan ya basu tabbacin cigaba da kyautata jin dadin alhazan.

Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya
Hajjin bana: An karrama Ganduje a kasar Saudiyya
Asali: Facebook

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya taya gwamnan Kano murnar samun wannan babbar nasara a sha’anin aikin Hajji.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Osun, Adegboyega Oyetola ya sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jahar don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1441.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamuis, 29 ga watan Agusta, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Zulhijja, daya samu sa hannun babban sakataren ma’aikatan cikin gida na jahar Osun, Adebisi Obawale.

Gwamnan ya taya al’ummar Musulmai murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, sa’annan ya yi kira ga Musulmai su dage da yi ma jahar Osun addu’o’in kariya, zaman lafiya, kwanciyar hankali, shugabanci nagari da samun cigaba mai daurewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng