Ba zan taba yin mataimakin gwamna ba – Dino Melaye

Ba zan taba yin mataimakin gwamna ba – Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya karyata cewar yana so ya fito a matsayin mataimakin gwamnan wani tsohon gwamnan jihar, Captain Idris Wada

- Melaye yace an shirya bayanin ne domin hana shi zama dan takarar jam’iyyar PDP, a zaben fidda gwani na gwamna da za a gudanar a ranar 3 ga watan Satumba

- Ya nemi jama'a da su yi watsi da batun

Sanata maiwakiltan yankin Kogi ta yamma, Dino Melaye ya karyata cewar yana so ya fito a matsayin mataimakin gwamnan wani tsohon gwamnan jihar, Captain Idris Wada.

A wani jawabi daga hannun hadiminsa a kafofin watsa labarai, Gideon Ayodele, a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, sanatan ya bayyana cewa an shirya bayanin ne domin hana Melaye zama dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben fidda gwani na gwamna da za a gudanar a ranar 3 ga watan Satumba.

“Captain Idris Wada ya fadi a zaben da ya gabata, inda ya sha kaye a hannun gwamna mai mulki sannan hakan ba zai yi wani ma’ana ba cewa Dino Melaye, mutumin da ya fi shi dabaru da hangen nesa, zai tsaya a bayan irin wannan dan takara,” cewar jawabin.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye mai wakiltan mazabar Kogi ta Yamma na jihar Kogi inda ta bukaci a sake gudanar da sabon zabe kan dalilin kallubalantar nasararsa da akayi a kotu.

A bangarensa, Dino Melaye ya ce ko kadan hakan bai razana shi ba kuma yana da tabbacin cewa nasarar da ya samu tun farko tabbataciya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel