To fah: Abinda nake nema ba shi na gani ba, saboda haka na fita daga Kannywood - Jaruma Halima Abdulkadir

To fah: Abinda nake nema ba shi na gani ba, saboda haka na fita daga Kannywood - Jaruma Halima Abdulkadir

- Kyakkyawar jarumar fina-finan Hausa Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar ta bayyana cewa karshen zamanta a masana'antar Kannywood ya zo

- Inda ta ce abinda ta zo nema a masana'antar ba shi ta samu ba, sannan kuma abinda ta yi tunani ba shi ta gani ba

- Ta ce ita tunda ta fara harkar fim ba ta taba samun matsala da kowa ba, kuma babu wanda ya taba samun matsala da ita

Wani bidiyo da ya dinga yawo a shafukan sada zumunta ya bayyana yadda kyakkyawar jaruma Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar ta bayyana cewa ta fita kwata-kwata daga masana'antar Kannywood.

Ga dai abinda jarumar ta ce a cikin bidiyon:

"Assalamu Alaikum jama'a suna na Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar, ina so nayi amfani da wannan damar na sanar da jama'a da masoyana cewa daga ranar irin ta yau 29 ga watan Agustan shekarar 2019, ni ba 'yar fim bace ba, na fita daga masana'antar Kannywood."

KU KARANTA: Ga irinta nan: Ya taimaka mishi ya fito dashi daga rana ya sanya shi a inuwa, shi kuma ya jefa shi cikin ranar

"Kar mutane su dauka cewa wani abu ne marar kyau ya faru da ya sanya na fita, ba haka bane, tunda na shigo masana'antar nan ban taba samun wani tashin hankali da kowa ba, kawai dai wani daliline guda daya yasa na fita, abinda nayi tunanin zan gani a masana'antar ba shi na gani ba, abinda kuma nazo nema bashi na samu ba.

"Sannan ina rokon duk wanda na yiwa laifi ya yafe mini, nima kuma na yafewa kowa da kowa, na gode."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng