Rashin sani: Yadda za a iya maganin satar mutane (Kidnapping) ta hanyar amfani da manhajar 'Whatsapp'

Rashin sani: Yadda za a iya maganin satar mutane (Kidnapping) ta hanyar amfani da manhajar 'Whatsapp'

Legit.ng Hausa ta ci karo da wani rubutu mai ma'ana da muhimmanci ga dukkan jama'a da wani bawan Allah, Mahmud Labaran Galadanchi, ya yi a kan yadda mutane zasu iya amfani da wayoyinsu na hannu (smartphones) domin yin maganin satar mutane (Kidnapping).

Ga abinda Galadanchi ya rubuta kuma ya roki jama'a su yada domin kowa ya sani; "da yawan mutane suna siyan wayoyin hannu ne ba don abunda wayoyin suka kunsa ba (facilities) sai don ado ko burgewa. Wani har ya jima da wayar tasa baya iya sanin wata bukata ta musamman da wayar zata iya yi masa a al'amuran sa na yau da gobe. Waya ta shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan Adam har da tsaron rayuka da gujewa fadawa hadari kamar kidnapping. Da yawan mutane suna amfani da applications na wayoyin su amma basu gama kewayewa da abubuwan da wannan applications zasu amfane su ba.

Wani zai iya tambayar kan sa ta yaya zan iya maganin kidnapping ko satar mutum ta hanyar amfani da wayar hannu? Wannan abu ne mai sauki kuma mai saukin ganewa. A yanzu mafi yawan masu amfani da wayoyi suna yin watsapp. Ta hanyar amfani da watsapp zaka iya maganin kidnapping ko da anyi kidnapping naka za'a iya gane a inda kake cikin sauki. Yadda zaka yi hakan shine:

1. Ka kunna "location" na wayar ka.

2. Ka shiga watsapp application ka zabi wanda kake so ka yiwa sharing location din.

3. A kasa, inda kake sharing hotuna zaka ga option na "location" sai ka shiga zaka ga yana detecting current location din kake a wannan lokacin. Bayan ya gama zai nuna maka unguwar da kake a map.

DUBA WANNAN: Rashin tsaro bai dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna ba - Rundunar 'yan sanda

Daga nan kana da zabi guda biyu. Zaka iya sending current location din da kake ko kuma kayi sharing live location. Banbancin na farko da na biyun shine:

Sending current location: shine ka turawa wani inda kake a wannan Lokaci. Wannan zai taimaka idan aka kama mutum baa san inda yake ba. Idan ya turawa wani location din za'a gane wajen da yake ba tare da shan wahala ba.

Sharing live location: in ka zabi wannan kuma, duk wanda ka turawa wannan lokaction din zai rika ganin duk inda kake a map din. Misali ka taho daga Kano, sai ka yiwa wani sharing live location din ka a kaduna, duk inda kake yana gani a nasa map din kuma yana tracing din ka. Wannan zai taimaka shima wajen gane inda mutum yake. Zai fi taimakawa jami'an tsaro wajen sanin matakin da zasu dauka. Amma kai zaka fara taimakawa kan ka duk sanda zaka yi tafiya mai tsayi kayi sharing live location din ka da wani a wani garin don gudun faruwar wani abu mai kama da kidnapping.

Ina fatan mutanen mu zasu fara amfani da wannan dabara. Shi watsapp ba wai iya chatting kawai ake ba harda irin wadannan muhimman al'amura wadanda suke taimakawa tsaron rayuwa da dukiyoyin al'umma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng