Albashina a matsayin Gwamnan jihar Oyo N650,000 ne rak – Seyi Makinde

Albashina a matsayin Gwamnan jihar Oyo N650,000 ne rak – Seyi Makinde

Seyi Makinde ya bayyana albashin da yake dauka a matsayin gwamnan jihar Oyo yayinda yake jawabi ga sabbin kwamishinonin da aka rantsar a jihar.

Gwamnan na jihar Oyo wanda ya nuna shirinsa na magance matsalar rashin biyan isasshen albashi a ma’akatun gwamnatin jihar, yace albashinsa a matsayin gwamnan jiha ya kasance N650,000 ne kacal.

Gwamna Seyi Makinde ya kuma bayyana yadda ya zata albashinsa zai kai kamar naira miliyan 3 zuwa miliyan 4 duk wata a lokacin da ya sanar da cewar zai bayar da dukka albashin nasa ga hukumar fansho a lokacin ratsar da shi.

Seyi ya yarda cewa babu mamaki shirin yaki da rashawa ya samu cikas ne a sanadiyar rashin biyan isasshen albashi yayinda ya bukaci kwamishinoni da su yi aiki don tabbatar da kudirinsa da shirinsa na kawo ci gaba a jihar Oyo.

Yace: “Ta yaya mutumin da ke karban $24,000 a shekara zai jagoranci kasafin kudi na dala milyan dari biyar? Dole zai kwadaitu da yawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Yahaya Bello ya lashe zaben fidda gwanin APC a jijar Kogi

“A lokacin da nake tasowa, a duk lokacinda nag a sakatarorin dindindin da manyan jami’an gwamnati, cikin manyan motocin jeep, sai nayi tunanin suna samun kudi ne sosai saboda ni ina tuka mota kirar Peugeot ko Toyota Camry.

“Amma a lokacin da na zo nan, albashin sakatarorin dindindin ya kasance kasa da N500,000 a wata, a wannan yanayi inda masu kwangila ke zuwa da manyan abubuwan kwadaitarwa. Sai dai za mu kawo mafita ga hakan, wanda shine kasuwanci ba yadda aka saba ba a jihar Oyo.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel