Kaduna: Gwamnatin jihar Yobe zata yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji

Kaduna: Gwamnatin jihar Yobe zata yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji

Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa zata yi wa dukkan malaman makarantun gwamnatin jihar jarrabawar gwaji.

A cikin wani jawabi da ta fitar ranar Laraba, gwamnatin jihar ta bayyana cewa zata dauki karin wasu sabbin malaman da suka cancanta.

Bayan batun daukan sabbin malaman, gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da tankade da rairaya a tsakanin malaman da ke koyar wa a makarantun jihar domin sanin irin cancantarsu da dacewarsu da aikin koyar wa.

Aikin dauka da tantance malaman makarantar na daga cikin shawarwarin da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin gyaran bangaren ilimi a jihar ya bayar. An kafa kwamitin ne yayin wani taron kwararru da gwmnatin jihar ta dauki nauyi domin tattauna hanyoyin da za a bi domin bunkasa bangaren ilimi a jihar.

DUBA WANNAN: Fariya: Wani dan Najeriya ya yi wa diyarsa shimfida da bandiran takardun Dalar Amurka (Bidiyo)

A cikin watan Yuli ne gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kira taron kwararru a bangaren ilimi bayan ya bayyana damuwarsa a kan tabarbarewar ilimi a jihar, musamman 'zubar gado' da daliban makarantun sakandiren jihar ke yi duk lokacin da sakamakon jarrabawar kammala makarantun sakandire ya fito.

Jihohin arewacin Najeriya da dama sun bayyana niyyarsu ta gudanar da jarrabawar gwaji ga malaman makarantun a jihohinsu, musamman makarantun Firamare, tun bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da 'tankade da rairaya' a tsakanin malaman da ke koyar wa a makarantun firamaren jihar.

Sai dai, har yanzu babu wata jiha data gudanar da jarrabawar gwajin a kan malaman makarantun ta kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng