Allah ya saka da alkhairi: Hadiza Gabon na sake ginawa tsohon da ruwan sama ya rushewa gida a jihar Yobe

Allah ya saka da alkhairi: Hadiza Gabon na sake ginawa tsohon da ruwan sama ya rushewa gida a jihar Yobe

- Fitacciyar jaruma Hadiza Gabon ta kara yin wani namijin kokari, wanda al'ummar duniya suka yaba da shi

- Jarumar ta saka a sake ginawa bawan Allan nan da ruwan sama ya cinye gidanshi a jihar Yobe sabon gida

- Yanzu haka aikin ginin gidan yayi nisa yayin da gidauniyar jarumar ta Instagram ta wallafa hotunan aikin a shafinta

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, kuma wacce tauraruwarta ke haskawa a wannan lokaci, Hadiza Gabon ta taimakawa tsohon nan da hotunanshi suka karade shafukan sada zumunta.

Jarumar wacce tayi kaurin suna wajen bayar da taimako ga mabukata da masu karamin karfi a jihohin arewa ta taimakawa tsohon ta hanyar sanyawa a gina masa sabon gida.

Dattijon bawan Allah mai suna Abba Babuga dake karamar hukumar Patiskum a jihar Yobe, ruwan sama yayi awon gaba da gidanshi a wani mamakon ruwa da aka tafka a kwanakin da suka gabata.

KU KARANTA: Tashin hankali: Limami ya yiwa mahaifiyarsa yankan rago a jihar Anambra

Dalilin wannan ruwane yasa dattijon fitowa waje lokacin da ya rasa me yake yi masa dadi a rayuwa ya tsugunna a tsakiyar ruwa mutane suka yi ta kallonshi suna sanya hotunansa a yanar gizo.

Shafin gidauniyar jaruma Hadiza Gabon din na Instagram shine ya wallafa hotunan lokacin da aka fara aikin sake ginawa Abba Babuga sabon gidanshi wanda ruwan ya cinye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel