Neymar: Mun kusa samun yarjejeniya da PSG – Inji Darektan Barcelona

Neymar: Mun kusa samun yarjejeniya da PSG – Inji Darektan Barcelona

Labari na zuwa mana cewa kawo yanzu a na daf da samun yarjejeniya tsakanin kungiyar Barcelona da kuma PSG a game da cinikin Neymar wanda a ke so ya dawo tsohon kulob din sa.

Wani daga cikin manyan Darektocin Barcelona, Javier Bordas ya tabbatar da cewa kungiyar ta kusa cin ma matsaya a cinikin da ta ke yi da kungiyar Paris Saint German watau PSG na Faransa.

A zaman farko da a ka yi da Wakilan kungiyoyin, an gaza kai ga wata yarjejeniya. Yanzu Barcelona ta nuna cewa ta na sa rai za a samu matsaya mai bullewa kafin a rufe kasuwar bana.

Javier Bordas, da Oscar Grau, Eric Abidal da kuma Andre Cury ne su ka tafi Birnin Faris a Ranar Talata, 27 ga Watan Agusta, 2019 domin ganawa da manyan kulob din PSG a kan Neymar Jr..

Bordas ya ke fadawa ‘yan jarida a filin jirgin sama na El Prat a Barcelona cewa: “Babu wata yarjejeniya yanzu tukuna a kasa. Har yanzu tattaunawa a ke yi, mu na gab da gama ciniki.”

KU KARANTA: Jose Mourinho ya ce ya gaji da zaman kashe-wando a gida

Ana sa rai cewa Bordas da Eric Abidal da sauran ‘yan tawagar na Sifen su kammala magana game da yadda ‘dan wasa Neymar Jr. zai koma tsohon kulob dinsa da ya bari shekaru biyu da su ka wuce.

Mun ji kishin-kishin din cewa Barcelona za ta biya fam miliyan €170. Barcelona za ta bada wannan kudi ne a cikin biya biyu. A yadda abubuwa su ke tafiya kungiyar PSG ta raina wannan tayi.

Akwai yiwuwar a hada da Ousmane Dembele da kuma Nelson Samedo a wannan ciniki. Har yanzu Andre Cury ya na Faransa inda ya ke cigaba da ganawa da Wakilan PSG a madadin Barcelona.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel