'Yan bindiga sun kone motocin Sojoji guda uku a Katsina

'Yan bindiga sun kone motocin Sojoji guda uku a Katsina

Wasu 'yan bindiga sun kone motocin sojoji guda uku yayin wata musayar wuta da suka yi da tawagar jami'an tsaro a kan hanyar zuwa Shimfida a karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Mata uku sun samu raunuka yayin musayar wuta da aka fafata a daren ranar Lahadi, kamar yadda majiyar 'yan sanda a jihar Katsina ta sanar.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bidigar sun kai hari tare da rufe hanyar da takarar dare.

Anas Gezawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ya ce rufe hanyar da 'yan bindigar suka yi ne ya kawo musayar wuta tsakanin su da jami'an tsaro.

"Sakamakon musayar wutar da aka yi ne 'yan bindigar suka kone motocin sojoji guda uku da ta jami'an 'civil defence' guda daya," a cewar Gezawa.

DUBA WANNAN: Matar aure ta kashe mijinta saboda ta koma gidan tsohon mijinta a Kebbi

Sannan ya kara da cewa lamarin ya ritsa da wata motar fasinjoji da ta debo 'yan kasuwar kauyen Shimfida.

Kazalika, ya bayyana cewa an garzaya da mata uku; Binta Umar, Jamila Ibrahim da Karima Musa, da suka samu rauni zuwa asibiti.

"Har yanzu jami'an mu basu bar yankin ba domin tabbatar da ganin cewa wani abu bai sake faruwa ba," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel