Tuna baya: Jaruman Arewa 5 da suka shiga dakin aure bara

Tuna baya: Jaruman Arewa 5 da suka shiga dakin aure bara

A wani rahoto da muka kalato daga jaridar Pulse.ng Hausa, mun yi waiwaye da ake yi wa lakabi da adon tafiya, kan wasu fitattun jaruman dandalin Kannywood na Arewa da suka shiga dakin aure a shekarar bara ta 2018.

Ga wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka yi aure bara:

1. Abida Muhammad: Babu shakka tsohuwar fitacciyar jaruma, Abida Muhammad, ta sake wani sabon aure bayan rasuwar mijinta na farko. A ranar Juma'a 26 ga watan Janairun 2018 ne aka daura aure Abida da sabon angonta, Mustapha Abubakar.

2. Sadiya Adam: An daura auren Sadiya tare da angonta, Alhaji Sanusi Ahmad a ranar Lahadi, 1 ga watan Afrilu cikin birnin Zazzau. Abokanan sana'arta na Kannywood da dama sun halarci bikin da ya samu shahara a zaurukan sada zumunta.

3. Sadiya Kabala: A ranar Asabar 14 ga watan Afrilu cikin babban masallacin Al-mannar da ke birnin Kaduna, aka daura auren Sadiya Kabala tare da angonta Ahmed Isah.

KARANTA KUMA: An kama mai sayar da kilishi da laifin zamba ta N2.2m a Legas

4. Aminu Dagash: Shima jarumi Dagash ya bi sahun sauran abokanan sana'arsa ta wasan kwaikwayo, yayin da aka daura aurensa a ranar 31 ga watan Maris na shekarar bara.

5. Sa'idu Muhammad: Shahararren jarumin fina-finan turanci wanda aka fi sani da Funkis Mallam, ya sake sabon aure bayan rabuwarsa da matar shi ta farko wadda suka samu 'da daya tilo.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel