Yansanda sun kama wata kasurgumar mace mai satar mutane a Legas

Yansanda sun kama wata kasurgumar mace mai satar mutane a Legas

Da kyar da sudin goshi jami’ar rundunar Yansandan jahar Legas suka kwaci wata mata mai satar mutane da nufin yin garkuwa dasu daga hannun jama’a bayan sun fusata har ta kai ga sun yi kokarin banka mata wuta, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar mai suna Damilohun Omowumi ta ci dukan banza a hannun jama’a, tare da yi mata tsirara a kan titin Matiminu unguwar Ijora Badia, inda suka zargeta da sace wani karamin yaro dan shekara 3 a ranar 21 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Katankatana: Wadume ya ambaci sunan gwamnan dake daukan nauyinsa yana ta’asa

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta dauke yaron ne daga kofar gidansu da sunan wai zai mata kwatancen wani wuri da bata gane ba, sai dai Allah Yasa dan uwan yaron na kusa, inda ya sanya ihu, tare da tara mata jama’a.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “An kamata ne a lokacin da take kokarin tserewa da yaron, amma sai dan uwansa ya saka ihu, hakan yasa mahaifiyarsu ta fito da gudu tana ihu ita ma, daga nan jama’a suka kama matar

“A kofar gidansu ta daukeshi da sunan wai zai nuna mata hanyar zuwa gidan wata Alhaja, kiris ya rage matasan unguwar su kasheta kafin zuwa Yansanda da suka ceceta.” Inji shi.

Shi ma kaakakin rundunar Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni sun fara binciken matar saboda sun fahimci tana da alaka da bacewar wasu jarirai, sa’annan ya kara da cewa zasu mikata gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da binciken.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel