Matar aure ta kashe mijinta saboda ta koma gidan tsohon mijinta a Kebbi

Matar aure ta kashe mijinta saboda ta koma gidan tsohon mijinta a Kebbi

Wata matar aure mai suna Auta Dogo Singe ta kashe mijinta mai suna Abdullahi Shaho a karamar hukumar Bagudu da ke jihar Kebbi don kawai tana son aurenta ya mutu domin ta koma gidan tsohon mijinta.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta hada baki da wasu mutane biyu; Sahabi Garba da Garba Hassan, domin ta kashe mijinta, Abdullahi Shaho, da suke zaman aure tare a kauyen Sabon Gari da ke yankin Illo.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar Kebbi, Garba Muhammad Danjuma, ya ce matar ta kashe mijinta ne saboda tana son koma wa gidan tsohon mijinta mai suna Idris Garba, mazaunin kauyen Tugar Bature a yankin Illo na karamar hukumar Bagudu.

Garba ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta kama matar tare da mutanen biyu da suka hada baki da ita domin aikata kisan.

DUBA WANNAN: Amina Zakari: Buhari ya bawa dan babbar ma'aikaciyar INEC mukami a gwamnatinsa

Kazalika, ya kara da cewa; "kwanan nan zamu gurfanar da dukkansu a gaban kotu."

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar 'yan sandan jihar na neman wasu mutane hudu; Yahuza Ibrahim, Murtala Abdullahi, Malam Nasiru da Dansilami bisa zarginsu da yi wa wani mutum, Adamu Yaro, fashin kudi N253,000 da babur na hawa kirar 'Hajoue' da wasu sauran kayansa masu daraja.

Ya ce mutanen, mazauna kauyen Gotomo a karamar hukumar Argungu, sun shiga gidan mutumin ta karfin tsiya dauke da muggan makamai tare da yi masa fashi a kauyen Kalgo.

A cewarsa, daga baya jami'an 'yan sanda na rundunar SARS da atisayen 'Puff Adder' sun samu nasarar cafke mutanen a maboyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel