Buhari ya bawa dan babbar ma'aikaciyar INEC mukami a gwamnatinsa

Buhari ya bawa dan babbar ma'aikaciyar INEC mukami a gwamnatinsa

A wani salo da wasu jama'a ke ganin tamkar sakayya ce ga samun nasararsa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada Mista Ahmad Rufai Zakari, da wurin tsohuwar hukumar zabe (INEC) ta rikon kwarya, Amina Zakari, a matsayin mai bashi shawara a kan aiyukan cigaban kasa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Ahmad Zakari ya mika sakon godiya ga shugaba Buhari a kan mukamin da ya bashi tare da bayyana cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen bawa gwamnatin Buhari gudunmawa.

"Ina godiya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a kan wannan dama da suka bani domin hidimtawa kasa. Wannan mukami ba nawa bane kadai, na dukkan matasan da basu kai shekaru 40 bane a duniya. Zan yi iyakar kokarina wajen ganin na sauke nauyin da aka dora min. Ina yi wa 'yan Najeriya godiya," kamar yadda Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Shugaba Buhari ya sha suka a lokacin da ya nada Amina Zakari a matsayin mukaddashin shugabar hukumar INEC.

DUBA WANNAN: Atiku ya 'fasa kwai' a kan dalilin da yasa Buhari ya fara binciken Obasanjo

Mista Adebayo Adebutu, wani mai hasashe a kan harkokin kasa, ya ce bawa Ahmad Zakari mukami ya tabbatar da zargin da ake yi a kan cewa Amina Zakari ta INEC 'yar uwa ce wurin shugaba Buhari.

Tun a ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 2015 jaridar 'Nigerian Tribune' ta wallafa rahoton cewa shugaba Buhari na da alaka ta jini da Amina Zakari.

Bayan jaridar ta Trinune ta wallafa wannan rahoto, ragowar kafafen yada labaran Najeriya sun kara wallafa labarin, lamarin da yaa Amina Zakari ta shaida wa gidan jaridar BBC cewa bata da wata alaka ta jini da shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel