Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa kasar Japan

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa kasar Japan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin jirgin sama na Haneda da ke Yokohama, kasar Japan domin halartan kasa da kasa na Tokyo akan ci gaban Afrika na bakwai.

Za a guda da taron mai taken ‘Africa and Yokohama, Sharing Passion for the Future’, a birnin Tokohama daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta.

A lokacin da ya isa kasar, mata da maza yan Japan cikin shigar gargajiya da aka fi yi a kasar Hausa sun yi wa shugaban kasar kyakyawar tarba.

Ana sanya ran shugaba Buhari zai dan yi tafiyar mota na yan mintuna kafin ya isa otel din Park Royal wanda aka tanadar ma shugabanni kasa da za su halarci taron.

Ana sanya ran taron zai mayar da hankali akan sabonta tattalin arzikin Afrika da kuma ci gaba yanayin kasuwancin yankin ta fannin zuba jari.

KU KARANTA KUMA: Da dumi dumi: Kotu ta aika sammaci ga AGF da EFCC kan dukiyar Yari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, shugaba Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Yokohama na kasar Japan domin wani halartar wani taron kasa da kasa da za a yi a ranar Laraba, 28 ga watan Agusta, 2019.

Za a yi taron ne a kan cigaban kasashen Afrika (CITAD), kuma wannan shine karo na bakwai da aka taba gudanar da taron tun da aka fara yinsa.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrazak Abdulrahman, na daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari zuwa taron na TICAD7.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel