A na zargin Direbobi da laifin sace wasu karafuna a matatar Dangote

A na zargin Direbobi da laifin sace wasu karafuna a matatar Dangote

Mun samu labari cewa wasu Direbobi biyu da ke aiki a kamfanin man Dangote a Najeriya sun samu kansu a gaban wani karamim kotun majistare da ke Legas inda a ke zargin su da laifin sata.

Kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto, a na zargin Ibrahim Madaki da Abokin aikinsa Mohammed Nuru ne da laifin sace wasu manyan rodin karafuna daga matatar man Dangote.

Kudin wadannan karafun da a ka sace a kasuwa ya kai Naira miliyan daya. A na zargin wadannan Direbobi na kamfanin da wannan danyan aiki ne a a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019.

Mai gabatar da kara a kotun Majistaren na Tinubu watau Ajaga Agboko ya bayyana cewa Direbobin nan sun sace karafun har 410 ne a harabar kamfanin da ke cikin yankin Ibeju-Lekki.

KU KARANTA: Karin bayani game da motocin yakin da a ka datse a Adamawa

Lauyan da ya shigar da kara ya fadawa Alkali cewa masu gadin kamfanin ne su ka kama Madaki da Nuru dumu-dumu bayan sun zuba karafunan a motocinsu har su na shirin tserewa cikin dare.

Da Alkali mai shari’a ya karantowa wadannan Direbobi laifinsu, sai su ka yi kememe su ka ce lallai ba su saci wannan kaya ba. Wannan ya sa kotu ta dage shari’a har sai cikin watan gobe.

Tuni aka bada belin Madaki mai shekara 20 da ‘Danuwan aikinsa Nuru mai shekaru 25 a Duniya. An bada belin wadanda a ke tuhuma ne a kan N200, 000 kafin a cigaba da shari’a a Satumba.

Fitaccen Attajirin nan na Afrika, Aliko Dangote, shi ne wanda ke gina wata katafiyar matatar danyan mai a Najeriya. Idan an gama wannan aiki, za a rika tace danyan man Najeriya a gida.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel