Ibo da Yarbawa su na iya rasa mulki a 2023 idan su ka raba-kan su – Inji Sani

Ibo da Yarbawa su na iya rasa mulki a 2023 idan su ka raba-kan su – Inji Sani

Mun ji cewa fitaccen Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci yankin jihar Kaduna a majalisar da ta shude ya fito ya yi magana game da zaben shugaban kasa da za a yi a Najeriya a shekarar 2023.

Shehu Sani ya bayyana cewa mutanen Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma za su iya shan kasa a zaben 2023 muddin ba su hada kan-su ba. Sanatan ya ce dole su guji raba-kai a zabe mai zuwa.

Tsohon ‘dan majalisar ya ke cewa dole ‘yan siyasan na Kudu su hadu su tsaya mutum guda a matsayin ‘dan takararsu a 2023. Sani ya yi wannan jawabi ne wajen wani taro da a ka yi jiya a Abuja.

Kungiyar NUJ ta ‘Yan Jarida na reshen babban birnin tarayya ne su ka shirya wannan zama a Garin Abuja a Ranar Asabar, 24 ga Watan Agusta, 2019. Sanatan ya na cikin wadanda su ka yi magana.

Jagoran na jam’iyyar PRP ya ke cewa: “Ba a yi wa sauran bangarorin kasar nan adalci ba idan wani bangare ya yi amfani da yawan al’ummarsa da fadin kasa wajen cigaba da rike mulki a Najeriya.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yabawa kwazon wani Gwamnan PDP

Sani ya cigaba da cewa: “...Su na sane cewa ba dinbin yawan jama’an su ba ne ya kawo su kan mulki. Abin da na yi amanna da shi, shi ne tsarin kama-kama, mulki ya rika zagayawa ko ina a Najeriya.”

“Abin da zan ce shi ne akwai yiwuwar ‘Dan Arewa ya sake zama shugaban kasa a 2023 idan Yamma da Gabas ba su shawo kan matsalolinsu ba.” Sani zai so ya ga mulki ya koma Kudu domin su taba.

A jawabin Sanatan ya nuna cewa da zarar wani Inyamuri ya zama shugaban kasa a Najeriya, an rusa surutun raba kasa sannan kuma ba za a kara tado batun yakin basasa da a ka yi a shekarun baya ba.

Har ila yau tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya na cewa: “Idan wata jam’iyya ta amince da kama-kama amma a ka samu wata ta ki yin na’am da wannan tsari, babu shakka za a samu matsala.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel