Ambaliyar ruwa ta ci kananan hukumomi 5 a birnin Yola

Ambaliyar ruwa ta ci kananan hukumomi 5 a birnin Yola

Biyo bayan wani ruwan sama na mamako da ya kwarara a ranakun Juma'a da Asabar, ambaliyar ruwa ta hargitsa kananan hukumomi hudu na jihar Adamawa da suka hadar da Yola ta Arewa, Yola ta Kudu, Girei, Shelleng da kuma Ganye.

Wannan mummunan ambaliyar ta jefa mazauna da gwamnatin jihar cikin halin kaka-nika-yi a yayin da hukumar ba da agajin gaggawa a jihar ta dukufa wajen tanadar matsungunni da sansanai ga wadanda suka rasa muhallansu.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa a jihar, Dr Muhammad Suleiman, ya bayar da shaidar wannan lamari inda a cewarsa an tanadi sansanin jin kai da tuni mutane 219 sun tsuguna cikinsa a garin Yolde Pate da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Asabar dangane da yadda ambaliyar ruwa ta dagula al'amura a birnin Yola, babban jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ya ce an taki babbar sa'a yayin da babu ko rai daya da aka rasa.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta fara sauke nauyin jin kai da ya rataya a wuyanta inda ta ke dawainiyar ciyar da wadanda suka rasa muhallansu.

Ambaliyar ruwan da ta auku a kananan hukumomi biyar a birnin Yola ta zo ne bayan mako daya daidai da al'ummomin wasu kananan hukumomi biyu a Arewacin jihar suka afka tarkon kunci na rashin samun damar shige da fice, a sanadiyar ambaliyar ruwa da ta yi awon gaba da wata gada da ke iyaka da sauran yankunan jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, mafiya yankunan jihar da ambaliyar ruwa ta yi wa babbar ta'asa a karamar hukumar Yola ta Arewa sun hadar Jambutu, Kofare, Bachure, Demsawo da kuma Nasarawo.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, ambaliyar ruwa da ta auku a sanadiyar saukar ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ta ci gidaje 400 a jihar Jigawa.

A baya-bayan nan, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na Najeriya, Injiya Mustapha Maihaja, ya ce jihohi 30 a kasar na fuskantar barazanar ambaliya a sanadiyar kusancin su da tekun Neja da na Benuwe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel