Mayakan Boko Haram sun yi wa mutane 12 yankan rago a Nijar
Mahukunta a kasar Nijar sun ce wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram ne sun hallaka mutane 12 a garin Gueskerou na jihar Diffa wanda ke iyaka da kasar Najeriya.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne mahara haye a kan babura, suka kai hari kauyen Lumana a yankin garin Gueskerou kamar yadda mazaunansa suka shaidawa manema labarai na BBC Hausa.
Bayan razanar da al'ummar garin ta hanyar harbe-harben harsashin bindiga saman iska, maharan sun kuma hallaka mutane 12 ta hanyar yankan rago da wukake, inda suka fice salin alin a sanadiyar rashin jami'an tsaro da za su mai da martani.
Hussaini Boucary, magajin garin Gueskerou, ya bayar da shaidar cewa an binne gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar ranar Asabar.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mummanan hari ya auku bayan kwana biyu kacal da aukuwar makamancinsa a kananan hukumomin Gubio da Magumeri na jihar Borno. Sai wanda ya auku da yammacin ranar Alhamis a kauyuka uku na karamar hukumar Konduga a jihar.
KARANTA KUMA: Babu wata alaka ta soyayya tsakani na da Ganduje - Sadiya Kabala
Mayakan Boko Haram sun kone gidaje 73 da kuma shaguna 28 a kauyukan karamar hukumar Konduga kamar yadda shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Borno, Hajiya Sabuwa Yabawa Kolo ta bayar a shaida.
A ranar Alhamis da ta gabata ne gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, yayi tattaki zuwa garin Abuja, inda ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara ta koken yadda hare-haren 'yan Boko Haram ke ci gaba da ta'azzara a jihar.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng