An kammala bincike kan Sojojin da su ka kashe ‘Yan Sandan Najeriya a Taraba

An kammala bincike kan Sojojin da su ka kashe ‘Yan Sandan Najeriya a Taraba

Mun samu labari cewa Mutum bakwai da a ka kafa domin su yi bincike a Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Garin Abuja game game da kisan wasu ‘yan sanda sun karkare aikin da a ka sa su.

Kamar yadda labari ya zo mana dazu nan, wannan kwamiti ya kammala duk binciken da ya ke yi, kuma zai mika rahoto zuwa gaban shugaban hafsun sojojin Najeriya, Janar Abayomi Olonisakin a makon gobe.

A Ranar Litinin, 26 ga Watan Agusta, 2019, a ke sa ran rahoton wannan kwamiti na musamman zai shiga hannun shugaban sojojin kasar. Akwai kuma alamun cewa wasu Sojoji za su samu kan su a matsala.

Labari ya zo mana daga majiya mai karfi cewa akwai wasu Jami’an Sojoji da ‘yan sanda da sunansu ya fito cikin marasa gaskiya a binciken. Har da wasu masu fararen hula a ka samu da aikata laifi.

Idan har hakan ta tabbata, hukuma za ta hukunta jami’an tsaro ne yadda ta saba ta hanyar kafa kotun musamman na Sojoji ko ‘yan sanda inda za a yi zama a yanke hukuncin da ka iya zama kora daga aiki.

KU KARANTA: Wadume ya bayyanawa Duniyar silar tsabar dukiyarsa

Kwamitin da a ka kafa ya kammala aiki ne a jiya Juma’a. Babban Soja, Rear Admiral Ibikunle Olaiya, shi ne ya jagoranci binciken tare da wasu Sojojin sama da na kasa da kuma ma’aikatan DSS da DIA.

An binciki wasu jami’an tsaro da zargin su na da hannu wajen tarkar-tarkar da a ke yi da Hassan Wadume wanda a ke zargi da laifin garkuwa da mutane. A dalilin kama shi ne har a ka rasa wasu ‘yan sanda.

Tuni dai an gama shake duk Jami’in da ke zargi da hannu a wannan lamari. Kamar yadda a ka saba a gidan soja, ofishin CDS zai karbi rahoton binciken sannan ya bayyanawa Duniya matakin da a ka dauka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel