Asiri ya tonu: An gano sana'ar da Boko Haram ke yi don samun kudin sayen makamai

Asiri ya tonu: An gano sana'ar da Boko Haram ke yi don samun kudin sayen makamai

Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole ta Sojojin Najeriya, da ke yaki da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Olusegun Adeniyi, ya ce rundunarsa za ta mayar da hankali kan dakile hanyoyin kudin Boko Haram.

Ya ce za su mayar da hankali wurin dakile kasuwancin sayar da kifi da 'yan ta'addan ke yi a ko ina a kasar nan.

Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma'a a Maiduguri kan motocci dauke da kifi da fatan dabobi da aka kwace a Borno bisa zargin masu kayan na kasuwanci da 'yan Boko Haram ne.

DUBA WANNAN: Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Adeneyi ya ce jami'an tsaro na NSCDC sun kama motocci hudu dauke da kifi a tittin Maiduguri zuwa Ngala. Ya ce sojojin ba su fice a jihar Borno ba sai dai sun canja salon yakinsu don kare afkuwar hari a sansanin su.

Ya ce sojojin sun rage shingen da suka kafa a cikin gari sun bullo da tawagar soji na gaggawa da ke yawo a gari don magance duk wata matsala da ta taso da ma kare afkuwar hakan.

Ya ce: "Boko Haram sun koma yin kasuwanci ne domin samun kudin sayen makamansu. Mun san akwai masu sana'ar su a Najeriya amma irin sayar da kifin da Boko Haram da bullo da shi na kawo hargitsi ne da kuma samun kudin cigaba da ta'addanci a Arewa maso Gabas."

"Duk wanda ya bari aka yi amfani da dokinsa ko rakumi don yi wa Boko Haram jigilar kifi shima ya na cikin 'yan ta'adda saboda yana taimaka musu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel