An kawata birnin Sokoto saboda bikin diyar Sarkin musulmi

An kawata birnin Sokoto saboda bikin diyar Sarkin musulmi

- An yi wa wurare daban-daban kwaskwarim a birnin Sokoto saboda bikin daurin auren diyar Sarkin Musulmi, Gimbiya Fatima

- Ana sa ran za a daura auren ne a fadar mai martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III da ke garin Sokoto

- Ana sa ran manyan baki daga gida Najeriya da kasashen ketare za su hallarci daurin auren Fatima Sa'ad Abubakar da Mahmoud Yuguda da za ayi a ranar Asabar

An yi wa manyan tittuna da shatale-tale na garin Sokoto kwaskwarima saboda shirin bikin daurin auren Gimbiya Fatima diyar Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar da za a gudanar a ranar Asabar.

Jagoran kwamitin shirye-shirye na bikin, Alhaji Tafida Sarkin Fadan Sokoto ya bayyana cewa an kafa kanananan kwamitoci domin tabbatar da gudanar da bikin cikin nasara.

DUBA WANNAN: Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Ya bukaci hadin kai al'umma domin ganin an gudanar da bikin lami lafiya duba da cewa ana sa ran manyan baki daga gida Najeriya har ma da kasashen ketare za su hallarci bikin.

Jagoran bikin ya yi kira ga al'ummar garin Sokoto su nuna halayensu na karamci da kamun kai da aka san su dashi a tarihi.

Ana sa ran za a gudanar da daurin auren Gimbiya Fatima Sa'ad Abubakar ne da angon ta Mahmoud Yuguda, dan tsohon gwamnan jihar Bauchi a fadar mai martaba Sarkin Musulmi da ke Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel