Tabbas ni na saka 'yan sanda suka kama Sadiya Haruna har sai da ta bada hakuri - In ji Teema Makamashi

Tabbas ni na saka 'yan sanda suka kama Sadiya Haruna har sai da ta bada hakuri - In ji Teema Makamashi

- Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Teema Makamashi ta fito ta tabbatar wa da jama'a cewa tabbas ita ce ta saka aka kama Sadiya Haruna

- A jiya ne dai Sadiya Haruna ta fito a cikin wani bidiyo take karyata cewar babu wasu jami'an tsaron da suka kamata

- Wannan dai duk ya samo asali ne bayan rikicin da ya barke tsakanin jaruman Kannywood din da ita Sadiya Haruna bayan ta ci musu mutunci

A irin wutar da take ta faman ruruwa a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood akan irin cin mutuncin da Sadiya Haruna ta yiwa wasu manyan jaruman masana'antar ta kai ga 'yan sanda sun kamata inda har ta kwana a wajensu, daga baya kuma suka saketa bayan ta bayar da hakuri.

Sai dai kuma Sadiya Haruna wacce ta yi suna a bangaren sanya bidiyo da maganganu na batsa a shafin sadarwa na Youtube, ta karyata wannan magana da mutane ke yi na cewa ana kamata.

Hakan ya sanya fitacciyar jaruma Teema Makamashi fitowa a cikin wani sabon bidiyo take tabbatarwa da mutane cewa tabbas ita ce ta saka aka kama Sadiya Haruna, kuma ba a saketa ba har sai da ta bayar da hakuri.

KU KARANTA: Tirkashi: Lokacin ina 'yar shekara takwas a duniya sai da kanin Kakana yayi lalata dani - Juliet Ibrahim

Ga abinda jarumar ta ce:

"Assalamu Alaikum, kamar dai yadda kuka sani sunana Teema Makamashi jakadiyar FKD, naji mutane suna ta faman tambayata akan abinda ya hada ni da Sadiya Haruna, kuma ita ma naji ta na karyata cewa an kamata.

"Na yi kararta wajen hukuma sun kamata sun binciketa ta kwana ta wuni a karshe ta bada hakuri komai ya riga ya wuce, amma kuma ta karyata cewar an kamata, kamata kam tabbas an kamata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel