Babu wata alaka ta soyayya tsakani na da Ganduje - Sadiya Kabala

Babu wata alaka ta soyayya tsakani na da Ganduje - Sadiya Kabala

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood 'yar asalin jihar Kaduna wadda Allah Khaliku ya zuba wa kyawun sura, Sadiya Kabala, tauraruwarta ta fara haskawa biyo bayan bayyanarta a matsayin agola a fim dinnan mai lakabin Korarriya.

Baya ga haka jarumar ta kara shahara a sanadiyar bayyanarta a wasu bidiyon wakoki da kuma na tallan siyasa da taya yakin neman zaben ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan lamari ya sanya jita-jita da rade-radi ke faman yaduwa kan zargin wata alaka ta soyayya da ta kullu a tsakaninta da gwamnan na Kano. Sai dai a yayin wata hira da Aliyu Askira, ta fayyace zare da abawa kan al'amuran da suka shafi sana'arta ta shirin fim da kuma kalubale da take fuskanta.

Dangane da soyayyar da ake zargin ta kullu a tsakaninta da gwamnan jihar Kano Ganduje, Sadiya ta ce babu kamshin gaskiya kan wannan zargi wanda a cewarta ya samo tushe ne daga wurin mahassada da kuma 'yan adawa.

Ta ce lamarin ya sanya ta yi amfani da zaurukan sada zumunta na zamani domin karyata wannan zargi da ake yi wanda ba ta da masaniyar inda ya samo asali, inda ta ke neman yafiyar gwamnan Kano da kuma mai dakinsa, Dakta Hafsatu Ganduje.

KARANTA KUMA: 'Yan Boko Haram sun kone gidaje 73 da shaguna 28 a Konduga - Zulum

Shahararriyar jarumar ta ce ta yi mamaki kwarai da aniya dangane da yadda wannan jita-jita ta samo asali, inda ta ce alakar da ta shiga tsakaninta da gwamnan na Kano ba ta wuce yi masa tallar zabe ba kuma ba za ta daina kyautata masa zato ba a matsayinsa na amintaccen jagora.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel