An kama shugaban makaranta da laifin neman matar aure a Kano

An kama shugaban makaranta da laifin neman matar aure a Kano

Wata kotun majistire da ke zamanta a birnin Kanon Dabo, ta bayar da umarnin tsare mataimakin shugaban kwalejin fasahar lafiya ta karamar hukumar Bebeji, a gidan kaso na tsawon kwanaki biyar bayan zarginsa da laifin neman wata dalibarsa da ta kasance matar aure.

Jaridar Kano Today ta ruwaito cewa, wannan mummunan lamari ya auku a yayin da mataimakin shugaban makarantar, Mas'ud Abdullahi, a watan gobe na Satumba zai fara aikin karantarwa a jami'ar gwamnatin tarayya ta birnin Dutse bayan ya kammala karantun digiri na uku.

Ana zargin Mista Abdullahi da neman biyan bukatarsa ta sha'awar 'da namiji da wannan mata inda zai musanya mata da maki a jarrabawa duk da kuwa yana da masaniyar akwai igiyar aure a kanta.

Bayan ya matsanta mata tare da bayyana kwazabarsa karara, rahotanni sun bayyana cewa dalibar ta amince da bukatarsa, kuma ta nemi ya garzaya gidanta na aure domin su yi bushashar su a can.

Mista Abdullahi ya shiga hannun hukuma a ranar Larabar da ta gabata, kuma an gurfanar da shi gaban kuliya a ranar Alhamis ta makon da ya shude.

KARANTA KUMA: An kama masu bautar kasa 6 na bogi a jihar Katsina

A yayin da Mista Abdullahi bai amsa zargin da ake masa ba, kotun bisa jagorancin Alkali Aminu Fagge, ta hau kujerar naki a kan bayar da beli, inda ta bayar da umarnin a tasa keyarsa zuwa gidan dan Kande tare da dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Agusta.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel