Wata sabuwa: Kwallon kafa halak ne a Musulunci - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Wata sabuwa: Kwallon kafa halak ne a Musulunci - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

- Shugaban majalisar malamai na jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa babu wani wuri a addinin Musulunci da ya ce wasan kwallon kafa haramun ne

- Ya bayyana cewa tarihi ya nuna cewa an fara wasan kwallon kafa fiye da shekaru dubu a duniya, kuma kasar Misira tana daya daga cikin kasashen da suka fara

- Ya ce da ace shi mai arziki ne da zai bude kungiyoyin kwallon kafa guda dari a Kano da za a dinga koyar da matasa kwallon kafa

Shugaban majalisar malamai na jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa babu in da aka haramta wasan ƙwallon ƙafa a addinin musulunci, sai dai kawai ana alaƙanta ƙwallon ƙafa da siyasar addini ne.

“Babu in da aka haramta wasan ƙwallon ƙafa a cikin addinin Musulunci, da ace ina da kuɗi to babu shakka zan buɗe ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 100 a faɗin jihar Kano.”

Sheikh Ibrahim Khalil ya ce tarihi ya nuna an fara wasan ƙwallon ƙafa fiye da shekaru dubu a duniya, kuma tun a lokacin ƙasashe irin su Misira su ka fara harkar.

KU KARANTA: Bidiyo: Tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Hafiz Ringim yana yi mini barazanar kisa akan hakkina - In ji wani dan Kano

Tun da farko shehin malamin ya bayyana hakan ne a filin wasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da ke unguwar sabon gari, a lokacin da ake gudanar da wasan sada zumunci tsakanin masu gabatar da labarin wasanni da kuma masu bugo waya.

“Babu abin da ya ke haɗa kan matasa fiye da ƙwallon ƙafa, kuma tana samar da zumunci tare da tabbatar da zaman lafiya.”

A karshe malamin ya ce a maimakon yara su dinga yawo kwararo-kwararo gwara a samar musu da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, yadda za’a dinga sayar da su a nahiyar turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel