Ma’aikata sun yi wa Zainab Shamsuna oyoyo bayan ta dawo ofis (Bidiyo)

Ma’aikata sun yi wa Zainab Shamsuna oyoyo bayan ta dawo ofis (Bidiyo)

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da gwamnatinsa inda ya nada Ministoci 43. Daga ciki akwai Zainab Shamsuna Ahmad wanda ta ka koma kan kujerar Ministar kudi.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, jama’a da-dama sun fito sun tarbi Hajiya Zainab Shamsuna a lokacin da ta isa ma’aikatarta. Shamsuna ta na cikin Ministocin da su ka dawo kan kujerunsu.

Shamsuna Ahmad ta samu tarba ta musamman daga ma’aikatan da ta bari a lokacin da aka rushe tsohuwar gwamnatin tarayya a karshen Watan Mayu bayan cikan wa’adin shugaba Buhari na farko.

Hajiya Shamsuna ta zama Ministar tattalin arzikin kasar ne shekara guda da ya wuce bayan da Misis Kemi Adeosun ta ajiye aikinta a Watan Satumban 2018 a dalilin zargin da a ka bijiro da shi a kan ta.

KU KARANTA: Akpabio ya bayyana abubuwan da zai yi a matsayin Ministan N/Delta

A wani bidiyo da Aisha Augie-Kuta ta saka a kafar sadarwa na Tuwita, an ga yadda ma’aikata su ka fito su na murnar dawowar Ministar ta su. Augie-Kuta ta saki wannan a shafin ta na @AishaAK49.

Ahmed na cikin Matan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba a cikin Ministocinsa wannan karo. Sauran matan sun hada da Sadiya Umar, Paul Tallen, Gbemisola Saraki da sauransu.

Wannan karo, Ministar za ta hada ma’aikatar kudi da kuma ma’aikatar kasafi da tsare-tsare. A farkon gwamnatin Buhari, Shamsuna ta yi aiki a matsayin karamar Ministar kasafin kasar na shekaru biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel