Babbar magana: Idan 'yan Hausa fim 'yan wuta ne to kowa ma dan wuta ne - In ji Ibrahim Mu'azzam

Babbar magana: Idan 'yan Hausa fim 'yan wuta ne to kowa ma dan wuta ne - In ji Ibrahim Mu'azzam

- Wani matashin saurayi mai amfani da shafin sadarwa na Facebook ya wallafa wani dogon rubutu a shafinsa wanda ya tada kura matuka a shafin na Facebook

- Matashin mai suna Ibrahim Mu'azzam Adam ya bayyana cewa idan har 'yan fim 'yan wuta ne to kowama dan wuta ne

- Ya ce kamar yadda kowa ke yin aikin zunubi haka shima dan fim yake yin aikin zunubi sannan kamar yadda kowa ke yin aikin lada haka shima dan fim yake yi

Wani matashi mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Ibrahim Mu'azzam Adam ya wallafa wani dogon rubutu da ya jawo kace nace a shafinsa, inda ya kalubalancin al'ummar dake kallon masu sana'ar shirya fina-finai da bata gari a cikin al'umma.

Matashin ya rubutu cewa: "In dai 'yan fim 'yan iskane to kowama dan iskane, idan 'yan fim fasikai ne kowama fasiki ne, idan kuma 'yan fim 'yan wuta ne hakazalika kowama dan wuta ne.

"Hujja ta a nan ita ce, wannan zamanin babu wanda baya kallon fim daga kan Malamai, Dalibai, Jahilai, masu hankali da mahaukata, idan kuma baka kallon Hausa fim kana kallon Indiya, ko America, idan ma baka kallon duka to kana sauraron wakokinsu, idan ma baka yi duka to kannanka ko yayyinka ko matanka suna yi.

KU KARANTA: Gargadi a kiyaye: Jerin jihohi 30 da ambaliyar ruwa zai shafa a Najeriya wannan shekarar

"Da dan fim da mai kallon fim duk uwar ubansu daya, duk inda Allah zai saka dan fim ranar lahira nan zai saka mai kallon fim. Saboda ba dan kuna siyan fim din kuna kalla ba da babu yadda za ayi su cigaba da yin fim din, dan haka baku da bambanci da su.

"Amma idan har za ayi adalci dan fim mutum ne tamkar kowa yadda kowa yake yin zunubi haka shima yake yinn zunubi yadda kowa yake yin aikin lada haka shima yake yin aikin lada."

Wannan jawabi na matashin ya tada hazo inda jama'a suka dinga tafka mahawara kan wannan lamari inda wasu ke gaskata zancensa suna kuma goyon bayan ra'ayinsa, yayin da wasu kuma ke sukar wannan ra'ayi na sa inda suke danganta hakan da rashin ilimi da wayewa.

Wannan dai duka na biyo bayan kura da ta tashi a cikin masana'antar ta Kannywood sakamakon kame dan cikinta da hukuma tayi bisa zargin yin bidiyo na rashin da'a wanda hakan ta sanya wasu manyan jarumai ficewa daga masana'antar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel