Ba mu san da kamun Wadume ba – Al’umman Layin Mai Allo

Ba mu san da kamun Wadume ba – Al’umman Layin Mai Allo

Har yanzu mazauna Hotoro Layin Mai Allo da Yandodo Hotorol a yankin karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano, na cike da mamaki akan kamun Hamisu Bala Wadume, wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da akayi a makwabtansu.

An tasa keyar Wadume, wanda aka kama a mafakarsa da ke Hotoro Layin Mai Allo, zuwa hedkwatar tsaro da ke Abuja domin amsa tambayoyi.

Majiyarmu wacce ta kai ziyara Layin Mai Allo, tayi Magana da mazauna yankin da dama wadanda suka ce basu san da kasancewarsa a yankinba da kuma kamunsa da jami’an tsaro suka yi.

Wani mai tireda yace: “Bani da masaniya akan kowani kamu da aka yi a wannan yankin."

Makwabcinsa, Malam Mohammed Idris, yace kawai jin labarin yayi a gidan rediyo sannan kuma cewa ya yi mamaki matuka da ya gane cewa dan ta’addan na buya ne a yankinsu.

KU KARANTA KUMA: Jirgin sama ke sauke wa ubangidana makamai a cikin jeji – Dan fashi

“Ka gane babu ta yadda za a yi mutum kawai ya san abunda ke gudana, idan da a ce an ji karar harbi ne, da hakan zai jawo hankalinmu amma tunda jami’an sun gudanar da lamarin ne cikin sirri babu yadda mutane za su san da lamarin,” inji shi.

Hajiya Aisha Abubakar tace hatta da mata da ke gida basu san da aikinba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel