Rundunar 'yan sanda ta kama jami'anta 4 da ake zargi da aikata kisan kai (Hoto)

Rundunar 'yan sanda ta kama jami'anta 4 da ake zargi da aikata kisan kai (Hoto)

Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta sanar da kama wasu jami'anta hudu da ake zargi da kisan wasu 'yan fashi biyu yayin da ake tsare da su.

Za a gurfanar da 'yan sandan hudu; Insifekta Fabiyi Omomayara, Saja Olaniyi Solomon, Saja Solomon Sunday da Kofural Aliyu Mukaila, a gaban kotu bisa tuhumarsu da saba dokar aiki da amfani da makami ta hanyar da bata dace ba.

A wani faifan bidiyo da ya mamaye kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta, an ga jami'an 'yan sandan sun bude wuta a kan 'yan fashin da ake kyautata zaton mambobin kungiyar 'Iba' ne.

Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum ne mai suna Valentine Anugu ya kira 'yan sandan da misalin karfe 3:00 na ranar 19 ga watan Agusta bayan wasu mutane hudu a kan babura guda biyu sun yi masa fashin wayarsa ta hannu da kudinta ya kai N450,000.

DUBA WANNAN: An gurfanar da wasu mutane 2 da suka sace mota bayan ta yi hatsari

'Yan sandan sun yi nasarar kama biyu daga cikin 'yan fashin tare da kwace musu bindiga da sauran makamansu kafin daga bisani su harbe su a cikin wata motar fasinjoji da suka fita aiki a cikin ta.

Da yake Alla-wadai da halayyar 'yan sandan, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya ce jami'an sun wuce makadi da rawa ta hanyar kashe masu laifi bayan sun kama su.

A cewar Elkanah, "duk da kasancewar 'yan fashin sun yi kaurin suna wajen aikata laifukan ta'addanci a yankin, jami'an sun nuna zake wa a nasarar da suka samu, sun wuce makadi da rawa ta hanyar kashe masu laifin."

Elkana ya kara da cewa rundunar 'yan sanda za ta cigaba da sanar da jama'a yadda shari'ar jami'an za ta kasance bayan an gurfanar da su a gaban kotu.

Rundunar 'yan sanda ta kama jami'anta 4 da ake zargi da aikata kisan kai (Hoto)
Jami'an 'yan sandan da ake zargi da aikata kisan kai
Asali: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng