Bidiyon yadda wani Malamin Jami'ar Maiduguri ya tilasta dalibai su rike miciji da ranshi kafin ya bari su ci jarrabawarshi

Bidiyon yadda wani Malamin Jami'ar Maiduguri ya tilasta dalibai su rike miciji da ranshi kafin ya bari su ci jarrabawarshi

- Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta ya bayyana yadda wani Malamin Jami'ar Maiduguri dake jihar Borno ya sanya dalibansa yin wani abu mai ban tsoro

- Malamin ya tilasta dalibansa akan dole sai sun dauki miciji da ranshi kafin ya hayar da su jarrabawarshi ta wannan zangon

- Daliban dai an bayyana cewa suna karatu ne a fannin namun daji, da halayensu, inda hakan yake nuna cewa dole daliban su saba da irin wannan dabbobi

Wani Malamin Jami'ar Maiduguri dake jihar Borno ya umarci dalibanshi da suke karatu a bangaren namun daji da su dauki miciji da ranshi kafin su samu su haye jarrabawarshi.

An nuno wasu daga cikin daliban yadda suke yin karkarwa wajen rike micijin inda shi kuma Malamin ya nuna ko a jikinsa, domin ya mayar da abin kamar doka akan kowanne dalibi sai ya dauka.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan sanda sun bankado wani katafaren gida da tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha ya bai wa wata budurwarsa 'yar Ethiopia

Wasu sun bayyana cewa micijin irin wannan gamsheka dinnan ce wacce take zama a cikin dutse, wadda ake ganin cewa bata da dafi kuma bata yiwa mutane komai, saboda haka dole dalibai da suke karatu a wannan fannin su saba da mu'amala da irin wannan namun daji.

Masana sun nuna cewa wannan abu da malamin yayi ba komai bane domin kuwa hanyace ta koyarwa kuma dama kalar wannan miciji ba mai cutar da al'umma bane, dan haka idan har dalibi yana karatu a wannan fanni dole ya saba da ire-iren wannan dabbobi koda ace zai gansu a wani wuri zai san hanyar da zai bullo musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel