Inuwa Kashifu ya zama Shugaban hukumar NITDA a Najeriya

Inuwa Kashifu ya zama Shugaban hukumar NITDA a Najeriya

Bayan nada Dr, Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Minista, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nada Inuwa Kashifu Abdullahi a matsayin shugaban hukumar NITDA na kasa.

Jama’a za su so ji wanene wannan Bawan Allah da ya canji Isa Pantami. Legit Hausa ta tsakuro tarihinsa:

1. An haifi Inuwa Kashifu Abdullahi ne a Fabrairun 1980 a Garin Hadejia a jihar Jigawa. Wannan Bawan Allah ya na da shekaru 39 kenan yanzu a Duniya.

2. Inuwa Kashifu ya yi Digirinsa na farko ne a Jami’ar fasaha ta Abubakar Tafawa Balewa. Ya kuma yi karatu a babbar jami’ar nan ta fasaha ta Duniya Massachusetts.

3. Malam Inuwa Kashifu Abdullahi ya yi karatu na kwas-kwas da-dama a gida da kasashen ketare irin su CISCO inda ya samu gogewa a kan fannin fasahar gafaka.

KU KARANTA: Wani Fitaccen Farfesan Najeriya ya ci gasar Duniya a kasar waje

Inuwa Kashifu ya zama Shugaban hukumar NITDA a Najeriya
Malam Inuwa Kashifu ya dare kan kujerar hukumar NITDA
Asali: Instagram

4. Sabon shugaban na NITDA ya yi fiye da shekaru 14 ya na aiki a Duniya. Daga ciki inda ya yi aiki akwai Galaxy Backbone na shekaru kusan 10 daga 2004 zuwa 2013.

5. A shekarar 2014 ne Inuwa Kashifu ya koma aiki a babban bankin Najeriya na CBN inda a nan tsohon Shugaban NITDA na kasa, Isa Ali Pantami ya hango shi.

6. A 2017, Dr. Isa Ali Pantami ya nada Malam Inuwa Kashifu a matsayin Mai ba shi shawara na musamman domin dabbaka wasu tsare-tsaren fasaha a fadin Najeriya.

7. Inuwa ya yi ayyuka barkatai a lokacin da ya yi aiki da Mai gidansa Dr. Isa Pantami. Wannan ya jawo ya samu lambobin yabo iri-iri. Sabon DG na NITDA ya na da aure da ‘Ya ‘ya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel